daga
Dakta
Almustapha Wali Sambo, MLAN
Digirin Farko a
fannin Hausa (B.A. Hausa) yana bayar da horo mai zurfi a fannonin ilimin harshe
da adabi da fassara da kuma nazarin al’adu. Kasancewar Hausa ɗaya daga cikin
manyan harsunan Chadi da aka fi magana da su a faɗin Yammaci da Tsakiyar Afirka,
kuma babban harshen hulɗa na yanki (lingua franca), masu wannan digiri suna da
ƙwarewar da ake buƙata ƙwarai a fannonin gwamnati da na masu zaman kansu da
kuma hukumomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Saboda haka, karanta wannan fanni na
Hausa yana samar da guraben ayyuka masu yawa sosai fiye da yadda wasu mutane
suke tsammani. Muhimman guraben ayyukan sun haɗa da:
1. Kafofin Yaɗa Labarai da Aikin Jarida
Ɓangaren yaɗa
labarai na ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar masu digirin Hausa aiki, kama
daga gidajen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da na cikin ƙasa baki ɗaya, har ma da
na jihohi.
- Gidajen Yaɗa Labarai na Ƙasa da Ƙasa: Mai
digiri a fannin Hausa zai iya kasancewa mai ba da rahoton labarai ko
marubucin labarai ko mai shirya shirye-shirye ko mai gabatarwa a gidajen
yaɗa labarai irin su BBC Hausa da Muryar Amurka (VOA Hausa) da Deutsche
Welle (DW Hausa) da Radio France Internationale (RFI) da kuma China Media
Group (CMG), wato Rediyon Ƙasar Sin.
- Kafofin Yaɗa Labarai na Ƙasa da na Yanki: Zai kuma
iya yin ayyuka a gidajen rediyo da talabijin na ƙasa da na jihohi (kamar
NTA, FRCN, AIT, da gidajen rediyo da talabijin na jihohi daban-daban) da
kuma gidajen rediyo/talabijin masu zaman kansu a faɗin Arewacin Najeriya.
- Gidajen Jaridu da Yaɗa Labarai a Kafar
Intanet: Zai iya kasancewa marubucin maƙaloli ko
edita ko ɗan jarida mai kawo rahotanni ga jaridun harshen gida (kamar
jaridar Aminiya) da sauran shafukan labarai na intanet.
- Sanya Fassarar Rubutu a Fim (Subtitling),
Canja Muryar Fim (Dubbing), da Shigar da Murya (Voiceover): Samar da
muryoyin fassara da rubutun shirye-shirye don masana’antar fina-finan
Hausa (Kannywood) da fina-finai masu faɗakarwa (documentary) da kuma
tallace-tallace.
2. Fasahar
Zamani da Harshe, Ƙirƙirarriyar Basira (AI), da Daidaita Fasaha da Harshe
Sakamakon
saurin haɓakar fasahar sarrafa harshe ta na'ura mai ƙwaƙwalwa (NLP) da tantance
murya ko magana da da kuma yaɗuwar fasahar sadarwa ta duniya, kamfanonin fasaha
suna neman masana harshen uwa ruwa-a-jallo. Saboda haka, wanda ya yi nazarin Hausa
a matakin digiri zai iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan da ke ƙasa ko duka:
- Ƙwararre kan Daidaita Fasaha da Harshe
(Localization Specialist): Fassara da daidaita manhajojin kwamfuta
da manhajojin waya da shafukan intanet da tsarin aiwatarwa na manhajoji
zuwa harshen Hausa don kamfanonin fasaha na duniya da sabbin kamfanonin
fasaha na Afurka.
- Mai Koyar da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) da
Tace Bayanai (Data Annotation): Yin aiki kan sarrafa rubutu zuwa murya
(TTS) da tantance murya kaitsaye (ASR) da tattarawa tare da tace bayanan
horar da manyan samfuran harsuna na na'ura mai ƙwaƙwalwa (LLMs) a harshen
Hausa.
- Masanin Kalmomi da Ƙamus (Terminologist
& Lexicographer): Samar da karɓaɓɓun kalmomin fasaha da
ƙamusai da fihirisar kalmomi don manhajojin intanet da na ilimi.
3. Fassara,
Tafinta, da Hulɗar Ƙasa da Ƙasa
Wanda ya
karanta Hausa zai iya kasancewa:
- Kwararren Mai Fassara/Tafinta: Yin
fassarar magana take-yanke (simultaneous) ko a jinkirce (consecutive), da
kuma fassarar takardu ga ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa
(INGOs) da hukumomin diflomasiyya da ofisoshin jakadanci da ƙungiyoyin
agajin jinƙai (misali hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, ICRC, MSF, USAID,
FCDO).
- Mai Fassarar Shari'a a Kotu: Taimaka
wa fannin shari'a da hukumomin tsaro da kwamitocin sasanta rigingimu ta
hanyar yin tafinta da fassara rubutattun bayanai da naɗiyar murya.
- Mai Fassarar Kasuwanci da Masana'antu: Fassarar
littattafan jagorar amfani da kayayyaki da bayanan magunguna da
tallace-tallacen kamfanoni da ƙa'idodin harkokin kuɗi na kamfanoni masu
rassa a ƙasashe daban-daban.
4. Ilimi, Tsara
Manhajar Karatu, da Aikin Koyarwa
Wanda ya
karanta Hausa zai iya kasancewa:
- Koyarwa a Makarantun Sakandare: Koyar da
harshen Hausa da adabi da al’adu a makarantun sakandare na gwamnati da
masu zaman kansu.
- Koyarwa a Makarantun Gaba da Sakandare: Yin aiki
a matsayin mataimakin mai koyarwa (Graduate Assistant) ko malami a
jami'o'i (universities) da kwalejojin fasaha (polytechnics) da kwalejojin
ilimi (colleges of education).
- Rubuta Littattafai da Tsara Manhaja: Haɗin
gwiwa da hukumomin kula da ilimi (kamar NERDC, SUBEB) da gidajen buga
littattafai don samar da kayayyakin koyarwa da littattafan karatu da
manhajojin koyar da ƙa'idodin rubutu da nahawu.
5. Buga
Littattafai da Fasahar Rubutu
Wanda ya
karanta Hausa zai iya kasancewa:
- Mai Buga Littattafai: Aiki a
matsayin editan tace rubutattun ayyuka (manuscript editor) da mai gyaran
kuskure (proofreader) ko editan karɓar ayyuka a gidajen wallafe-wallafe
masu buga littattafan ilimi na adabi ko na addini.
- Mai Ƙirƙirar Rubutu da Tsara Wasan
Kwaikwayo (Scriptwriting): Rubuta littattafan ƙagaggun labarai da
waƙoƙi da wasannin kwaikwayo da tsara rubutun fina-finai don gidajen buga
littattafai da wasannin dandamali da kafofin shirya fina-finai.
- Mai Ba da Shawarwari kan Al'adu: Ba da
shawarwari ga kamfanonin shirya fina-finai da kamfanonin tallace-tallace
da manyan kamfanoni dangane da sarrafa harshe daidai da fahimtar al'ada da
kiyaye abubuwan da al'ada ta haramta ko ta girmama.
6. Aikin
Gwamnati, Tsaro, da Leƙen Asiri
Wanda ya
karanta Hausa zai iya kasancewa:
- Mai Hulɗa da Jama'a da Aikin Farar Hula: Jami'in
yaɗa labarai ko jami'in hulɗa da jama'a ko jami'in tsare-tsaren tarurruka
(protocol officer) a ma'aikatun tarayya da na jihohi da ke kula da labarai
da al'adu da yawon buɗe ido.
- Mai Aikin Tsaro da Leƙen Asiri: Ayyukan
bincike da fassara da rubuta bayanan da aka bayar a magana da nazarin
bayanai a hukumomin tsaro da leƙen asiri (kamar NIA, DSS, hukumar leƙen
asirin soji da jami'an tsaron kan iyaka).
- Ma’aikaci a Cibiyoyin Al'adu da Tarihi: Ayyuka a
majalisun fasaha da al'adu na ƙasa da na jihohi da ɗakunan adana bayanai
na tarihi (archives) da gidajen ajiye kayan tarihi (museums) da hukumomin
kare kayan gado na ƙasa.
Ƙwarewar da Ke
Ƙara Buɗe Ƙofofin Samun Aiki
Amma fa a sani
cewa, domin samun mafi yawan manyan guraben ayyuka da aka bayyana a sama — musamman
a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kafofin yaɗa labarai da kamfanonin fasaha —yana da
muhimmanci sosai masu digiri su haɗa karatunsu da:
- Takaddun shaida na ƙwarewa a fannin
fassara da tafinta (misali daga ƙungiyoyi irin su CIOL, ATA, ko hukumomin
fassara na ƙasa irin su NITI).
- Ƙwarewa wajen amfani da kayan aikin
fasahar zamani da manhajojin taimaka wa fassara (CAT tools kamar su SDL
Trados, MemoQ) da manhajojin sarrafa rumbun bayanan harshe (corpus
management software).
- Nuna ƙwarewa mai zurfi wajen rubutu a
harsuna biyu ko fiye (misali haɗa babban matakin ƙwarewa a harshen Ingilishi
tare da ƙwarewar asali a rubutu da karatun Hausa, gami da rubutun Boko da
na Ajami).

No comments:
Post a Comment