ANYA! ZAN SAMI AIKI, IDAN NA YI DIGIRI A HAUSA?




 ANYA! ZAN SAMI AIKI, IDAN NA YI DIGIRI A HAUSA?

daga

Dakta Almustapha Wali Sambo, MLAN

 

Digirin Farko a fannin Hausa (B.A. Hausa) yana bayar da horo mai zurfi a fannonin ilimin harshe da adabi da fassara da kuma nazarin al’adu. Kasancewar Hausa ɗaya daga cikin manyan harsunan Chadi da aka fi magana da su a faɗin Yammaci da Tsakiyar Afirka, kuma babban harshen hulɗa na yanki (lingua franca), masu wannan digiri suna da ƙwarewar da ake buƙata ƙwarai a fannonin gwamnati da na masu zaman kansu da kuma hukumomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Saboda haka, karanta wannan fanni na Hausa yana samar da guraben ayyuka masu yawa sosai fiye da yadda wasu mutane suke tsammani. Muhimman guraben ayyukan sun haɗa da:

1. Kafofin Yaɗa Labarai da Aikin Jarida

Ɓangaren yaɗa labarai na ɗaya daga cikin manyan masu ɗaukar masu digirin Hausa aiki, kama daga gidajen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da na cikin ƙasa baki ɗaya, har ma da na jihohi.

  • Gidajen Yaɗa Labarai na Ƙasa da Ƙasa: Mai digiri a fannin Hausa zai iya kasancewa mai ba da rahoton labarai ko marubucin labarai ko mai shirya shirye-shirye ko mai gabatarwa a gidajen yaɗa labarai irin su BBC Hausa da Muryar Amurka (VOA Hausa) da Deutsche Welle (DW Hausa) da Radio France Internationale (RFI) da kuma China Media Group (CMG), wato Rediyon Ƙasar Sin.
  • Kafofin Yaɗa Labarai na Ƙasa da na Yanki: Zai kuma iya yin ayyuka a gidajen rediyo da talabijin na ƙasa da na jihohi (kamar NTA, FRCN, AIT, da gidajen rediyo da talabijin na jihohi daban-daban) da kuma gidajen rediyo/talabijin masu zaman kansu a faɗin Arewacin Najeriya.
  • Gidajen Jaridu da Yaɗa Labarai a Kafar Intanet: Zai iya kasancewa marubucin maƙaloli ko edita ko ɗan jarida mai kawo rahotanni ga jaridun harshen gida (kamar jaridar Aminiya) da sauran shafukan labarai na intanet.
  • Sanya Fassarar Rubutu a Fim (Subtitling), Canja Muryar Fim (Dubbing), da Shigar da Murya (Voiceover): Samar da muryoyin fassara da rubutun shirye-shirye don masana’antar fina-finan Hausa (Kannywood) da fina-finai masu faɗakarwa (documentary) da kuma tallace-tallace.

2. Fasahar Zamani da Harshe, Ƙirƙirarriyar Basira (AI), da Daidaita Fasaha da Harshe

Sakamakon saurin haɓakar fasahar sarrafa harshe ta na'ura mai ƙwaƙwalwa (NLP) da tantance murya ko magana da da kuma yaɗuwar fasahar sadarwa ta duniya, kamfanonin fasaha suna neman masana harshen uwa ruwa-a-jallo. Saboda haka, wanda ya yi nazarin Hausa a matakin digiri zai iya kasancewa ɗaya daga cikin waɗannan da ke ƙasa ko duka:

  • Ƙwararre kan Daidaita Fasaha da Harshe (Localization Specialist): Fassara da daidaita manhajojin kwamfuta da manhajojin waya da shafukan intanet da tsarin aiwatarwa na manhajoji zuwa harshen Hausa don kamfanonin fasaha na duniya da sabbin kamfanonin fasaha na Afurka.
  • Mai Koyar da Ƙirƙirarriyar Basira (AI) da Tace Bayanai (Data Annotation): Yin aiki kan sarrafa rubutu zuwa murya (TTS) da tantance murya kaitsaye (ASR) da tattarawa tare da tace bayanan horar da manyan samfuran harsuna na na'ura mai ƙwaƙwalwa (LLMs) a harshen Hausa.
  • Masanin Kalmomi da Ƙamus (Terminologist & Lexicographer): Samar da karɓaɓɓun kalmomin fasaha da ƙamusai da fihirisar kalmomi don manhajojin intanet da na ilimi.

3. Fassara, Tafinta, da Hulɗar Ƙasa da Ƙasa

Wanda ya karanta Hausa zai iya kasancewa:

  • Kwararren Mai Fassara/Tafinta: Yin fassarar magana take-yanke (simultaneous) ko a jinkirce (consecutive), da kuma fassarar takardu ga ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa (INGOs) da hukumomin diflomasiyya da ofisoshin jakadanci da ƙungiyoyin agajin jinƙai (misali hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, ICRC, MSF, USAID, FCDO).
  • Mai Fassarar Shari'a a Kotu: Taimaka wa fannin shari'a da hukumomin tsaro da kwamitocin sasanta rigingimu ta hanyar yin tafinta da fassara rubutattun bayanai da naɗiyar murya.
  • Mai Fassarar Kasuwanci da Masana'antu: Fassarar littattafan jagorar amfani da kayayyaki da bayanan magunguna da tallace-tallacen kamfanoni da ƙa'idodin harkokin kuɗi na kamfanoni masu rassa a ƙasashe daban-daban.

4. Ilimi, Tsara Manhajar Karatu, da Aikin Koyarwa

Wanda ya karanta Hausa zai iya kasancewa:

  • Koyarwa a Makarantun Sakandare: Koyar da harshen Hausa da adabi da al’adu a makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu.
  • Koyarwa a Makarantun Gaba da Sakandare: Yin aiki a matsayin mataimakin mai koyarwa (Graduate Assistant) ko malami a jami'o'i (universities) da kwalejojin fasaha (polytechnics) da kwalejojin ilimi (colleges of education).
  • Rubuta Littattafai da Tsara Manhaja: Haɗin gwiwa da hukumomin kula da ilimi (kamar NERDC, SUBEB) da gidajen buga littattafai don samar da kayayyakin koyarwa da littattafan karatu da manhajojin koyar da ƙa'idodin rubutu da nahawu.

5. Buga Littattafai da Fasahar Rubutu

Wanda ya karanta Hausa zai iya kasancewa:

  • Mai Buga Littattafai: Aiki a matsayin editan tace rubutattun ayyuka (manuscript editor) da mai gyaran kuskure (proofreader) ko editan karɓar ayyuka a gidajen wallafe-wallafe masu buga littattafan ilimi na adabi ko na addini.
  • Mai Ƙirƙirar Rubutu da Tsara Wasan Kwaikwayo (Scriptwriting): Rubuta littattafan ƙagaggun labarai da waƙoƙi da wasannin kwaikwayo da tsara rubutun fina-finai don gidajen buga littattafai da wasannin dandamali da kafofin shirya fina-finai.
  • Mai Ba da Shawarwari kan Al'adu: Ba da shawarwari ga kamfanonin shirya fina-finai da kamfanonin tallace-tallace da manyan kamfanoni dangane da sarrafa harshe daidai da fahimtar al'ada da kiyaye abubuwan da al'ada ta haramta ko ta girmama.

6. Aikin Gwamnati, Tsaro, da Leƙen Asiri

Wanda ya karanta Hausa zai iya kasancewa:

  • Mai Hulɗa da Jama'a da Aikin Farar Hula: Jami'in yaɗa labarai ko jami'in hulɗa da jama'a ko jami'in tsare-tsaren tarurruka (protocol officer) a ma'aikatun tarayya da na jihohi da ke kula da labarai da al'adu da yawon buɗe ido.
  • Mai Aikin Tsaro da Leƙen Asiri: Ayyukan bincike da fassara da rubuta bayanan da aka bayar a magana da nazarin bayanai a hukumomin tsaro da leƙen asiri (kamar NIA, DSS, hukumar leƙen asirin soji da jami'an tsaron kan iyaka).
  • Ma’aikaci a Cibiyoyin Al'adu da Tarihi: Ayyuka a majalisun fasaha da al'adu na ƙasa da na jihohi da ɗakunan adana bayanai na tarihi (archives) da gidajen ajiye kayan tarihi (museums) da hukumomin kare kayan gado na ƙasa.

Ƙwarewar da Ke Ƙara Buɗe Ƙofofin Samun Aiki

Amma fa a sani cewa, domin samun mafi yawan manyan guraben ayyuka da aka bayyana a sama — musamman a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da kafofin yaɗa labarai da kamfanonin fasaha —yana da muhimmanci sosai masu digiri su haɗa karatunsu da:

  • Takaddun shaida na ƙwarewa a fannin fassara da tafinta (misali daga ƙungiyoyi irin su CIOL, ATA, ko hukumomin fassara na ƙasa irin su NITI).
  • Ƙwarewa wajen amfani da kayan aikin fasahar zamani da manhajojin taimaka wa fassara (CAT tools kamar su SDL Trados, MemoQ) da manhajojin sarrafa rumbun bayanan harshe (corpus management software).
  • Nuna ƙwarewa mai zurfi wajen rubutu a harsuna biyu ko fiye (misali haɗa babban matakin ƙwarewa a harshen Ingilishi tare da ƙwarewar asali a rubutu da karatun Hausa, gami da rubutun Boko da na Ajami).

 

Taƙaitaccen Tarihin Sambo Wali da Ayyukansa

MUHAMMADU SAMBO WALI

(Malamin Makaranta, Masanin Tarihi, Marubuci Waƙoƙin Hausa)

daga

ALMUSTAPHA SAMBO WALI, PhD.

An haifi Muhammadu Sambo Wali a birnin Sakkwato, a ranar Jumu’a ta 9 ga watan Yuli, shekara ta 1937 Miladiyya. Wato daidai da 30 ga watan Rabi’u-Thani, shekara ta 1356 Hijiriyya. Sunan mahaifinsa shi ne Muhammadu Salisu. Mahaifiyarsa kuwa, sunanta A’ishatu. Bagimbane ne a wajen mahaifinsa. A wajen mahaifiyarsa kuwa Bafulatani ne. Ya rayu a gidan da aka san muhimmancin ilimi da tarihi musamman na sanin nasaba da salsala. Ɗa ne ga Muhammadu Salisu. Muhammadu Salisu ɗan Malam Yahya ne. Malam Yahaya ɗan Ahmadu ne, wanda aka fi sani da Ladan Ɗanhajara. Ahmadu ɗan Alƙalin Zamfara Muhammadu ne. Muhammadu ɗan Malam Abdussalami Bagimbane[1]  (almajirin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo) ne. Shi kuwa Abdussalami ɗan Malam Ibrahim ne. Malam Ibrahim ɗan Malam Shaharu ne (wanda ake kira Mallam Jaɓɓo Maigida Marannu). Malam Shaharu ɗan Mallam Hammadi Mai Babban Burgami ne, wanda gare shi Gobirawa suka ci birnin Alƙalawa[2].

Ta ɓangaren mahaifiyarsa kuwa, Bafulatani ne kamar yadda bayani ya gabata. Sunan mahaifiyarsa A’ishatu ɗiyar Marafan Wazirin Sakkwato Mallam Buhari, wanda aka fi sani da Marafa Tsoho. Shi kuwa Marafa Tsoho ɗan Waziri Sambo[3] (Ambo) ne. Waziri Sambo ɗan Ɗangaladima Ahmadu ne. Ɗangaladima Ahmadu ɗan Waziri Usman Giɗaɗo[4] (almajirin Shehu) da Nana Asma’u ne. Waziri Giɗaɗo ɗan Lema ne. Ita kuwa Nana Asma’u ɗiyar Shehu Usman ce. Usman ɗan Fodiyo ne. Fodiyo ɗan Usmanu ne. Shi kuwa Usmanu ɗan Salihu ne. Salihu ko ɗan Haruna ne. Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ne. Muhammadu Gurɗo ɗan Jaɓɓo ne. Jaɓɓo kuma ɗan Sambo ne. Shi kuwa Sambo ɗan Buba Baba ne. Buba Baba ɗan Baba Masarana ne. Baba Masarana ɗan Ayyuba ne. Shi ko Ayyuba ɗan Musa Jakollo ne. Shi kuwa Musa Jakollo ya fito ne daga Futa-Toro[5].

Sambo Wali ya yi karatu ga mahaifinsa. Kamar yadda ya bayyana cewa:

“Ina da kusan shekara shidda mahaihina ya’ aje aikin shari’a bisa ra’ayin kainai. Ba don an ce masa ya bar aiki ba. Ina da kusan shekara goma wani ƙaramin di’o[6] na Sakkwato wanda ake kira Mista Skinner[7] ya ɗauki mahaihina aiki dangane da yawon binciken wuraren tarihi yana biyanai albashi. Kuma mahaihina yana koya masa Hausa. A wannan lokacin, ya kasance mahaihina yana tahiya tare da ni saboda dalilin mahaihiyata ta rasu. Ko’ina za su na tare da ni yaka tahiya. Saboda haka, ga mahaihina niy yi karatun Ƙur’ani da kuma littahwan Lahallari da Ishimawi. A taƙaice, mahaihina shi yak koya min rubutun boko da lissahi. Sai a shekara ta 1955, ina ɗan shekara 18, yab bay yawo da ni, niz zauna gida Sakkwato.”

Ya ci gaba da karatun addini daga wajen malamansa irin su Malam Yahya Nawawi, Alƙalin Lardi da Malam Joɗi da Malam Maigandi Giɗaɗawa da Malam Babi Unguwar Dutsin Assada da Malam Sagware na Unguwar Alkanci da Malam Shayau na garin Kuci da kuma Waziri Junaidu, duk a cikin jahar Sakkwato ta yau. A kowane lokaci yakan tuna ire-iren nasihohin da waɗannan malamai suka yi masa. Kuma ya tabbatar da cewa, sun ba shi kyakkyawar tarbiyya. Allah ya saka musu da alheri, ya jiƙansu da rahamarsa.

Ta fuskar karatun boko kuwa, ba a bar shi a baya ba. Ya fara karatun ilimantare (firamare) a makarantar ‘Waziri Ward’, a shekarar 1945 miladiyya. A 1963 aka buɗa makarantar ‘Arabic Teachers’ College’ wadda a yanzu aka sani da ‘Abubakar Gummi Memorial Secondary School’ tare da shi yana a matsayin ɗalibi. A nan ne ya sami takardar shaidar kammala karatu mai daraja ta uku (Grade III). Haka kuma, daga baya ya sami takardar kammala karatu mai daraja ta biyu (Grade II) a nan makarantar. Daga nan ya tafi makarantar koyon Larabci, wato ‘School for Arabic Studies’ da ke Kano, inda ya yi kwas na sanin makamar aiki.

Sambo Wali ya fara aikin koyarwa a ‘Government Craft School’ da ke Sakkwato, a ranar 15 ga watan Satumba, shekara ta 1959. Ya ci gaba da koyarwa a makarantu daban-daban har zuwa shekarar 1978 miladiyya. A cikin shekarar 1978 ne Gwamnatin Tarayya ta neme shi da ya sauya aikinsa na malamin makaranta zuwa aikin jarida a sashen yaɗa labarai na Tarayya (NBC)[8] da ke Sakkwato. A inda ya karɓi kiran hukuma ya kama aiki da Gidan Rediyon Tarayya sashen jahar Sakkwato (Rima Radio[9]), tun daga 1978 har zuwa 1985. Ya riƙi shugabancin sashen al'amurran addini na gidan rediyon.

Irin hazaƙa da ƙwazon da yake da shi ne ya sa Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (na wancan lokaci), Farfesa Mahadi Adamu Ngaski ya neme shi da ya zo jami’ar, ya yi musu aiki. Ya kuma yarda. Inda ya bar aikin jarida ya dawo wa tsohon aikinsa, wato koyarwa da kuma bincike. Ya fara aiki da jami’ar a 1985, a Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci[10] ta jami’ar har zuwa 1996 a matsayin mai bincike, wato ‘researcher’. Kuma mai koyar da darussan da suka shafi addinin Musulunci. Daga wannan lokaci kuma, sai ya ajiye aikin gwamnati. Sai dai kuma Gidan Rediyon Rima sun sake nemansa a kan ya riƙa yi musu aiki na wucen-gadi. Inda yake kama musu a wani shiri da suke yi na faɗakarwa mai suna ‘Zauren Mai Anguwa’. Tun daga wancan lokaci (1996) har zuwa 2015[11] ana aiwatar da wannan shirin tare da shi. Sannan kuma, akan kira shi ‘Mallam Maiƙunƙuwa’ a cikin wannan shirin.

Sambo Wali ya yi zama wakilin hukuma da ƙungiyoyi da dama na ci gaban ƙasa da al’umma da kuma harshe. Ya kasance cikin kwamitin yaɗa al’adun gargajiya na jahar Sakkwato wanda gwamnatin jaha ta kafa a ƙarƙashin ma’aikatar al’adun gargajiya ta jahar Sakkwato, a shekarar 1976. Haka kuma, ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin wakilan da gwamnatin jahar Sakkwato ta naɗa na kwamitin samar wa almajirai da musakai wurin zama a shekarar 1979. Yana cikin ƙungiyar marubuta da manazarta waƙoƙin Hausa ta ƙasa. Sannan kuma ya taɓa zama shugabanta na jahar Sakkwato. Ya yi ta samun nasara a gasannin da ake yi na marubuta waƙoƙin Hausa. Ya sami lambobin karramawa da dama a kan wayar da kan al'umma daga matakai na jaha da ƙasa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Allah ya yi wa Sambo Wali baiwa ta rubutu, kuma rubutu na fasaha da hikima. Domin yana rubuta waƙoƙin Hausa tare kuma da rera su (yana kuma rera na Fulatanci). Haka kuma, yana rubuta tarihi musamman na Daular Usmaniyya da dangoginta tare kuma da sanar da al’umma shi. Ya fara waƙa tun yana ɗan shekara goma shaɗaya. Waƙar da ya fara yi ita ce waƙar ‘tsangwama da gungunin’ da abokan kwanansa yara ke yi masa, saboda yana tare da su, amma kuma ba sa’anninsa ne ba. Sai dai bai yi wa waƙar suna ba. Kuma ba ta da wani tsayayyen kari ko amsa-amo. Waƙarsa ta biyu da ya rubuta, ita ce waƙar ‘Ƙalubale ga Masu Sukar Shan Taba-gari[12] a kan irin tsaurara haramcin shan taba-gari (wadda ake saƙalewa a leɓe) da wasu mutane suka yi. A waƙar, ya nuna irin yadda ya yi da wasu mutane musamman ‘yan wazifan Jega da na Ƙauran-Namoda.

Ƙididdige waƙoƙin kowane marubuci waƙoƙi ko kuma mawaƙi abu ne mai matuƙar wahala. Domin ko shi marubuci waƙoƙin ko mawaƙin da wahala ya iya ƙayyade waƙoƙin da ya yi a rayuwarsa, sai dai kawai a yi ƙirdado, wato a kimanta. Saboda haka, ko shi Sambo Wali bai san adadin yawan waƙoƙin da ya rubuta ba.Ya dai tabbatar da cewa, ya rubuta waƙoƙi da dama a kan fannoni rayuwar al’umma. Waƙoƙin da ya fi rubutawa su ne waɗanda suka shafi wayar da kan al’umma a kan wata matsala da take gudana. Haka kuma, ya rubuta waƙoƙin da suka shafi yabo da nasiha da wa’azi da siyasa da gargaɗi da sha’awa da kuma tallace-tallace. Gwamnatin jaha ko ta tarayya ko ƙungiyoyi masu zaman kansu kan nemi Muhammadu Sambo Wali ya rubuta musu waƙa (tare da rera ta a kafafen yaɗa labarai ko tarurruka) a kan duk wani ƙuduri ko manufar da suke son isarwa ga al’umma.

Sambo Wali bai tsaya a kan waƙoƙi kaɗai ba. Domin masanin tarihi ne, musamman tarihin da ya shafi Daular Usmaniyya da ƙasashen Kabi da Gobir. Saboda ya yi rubutun tarihi da dama wanɗanda suka shafi waɗannan ƙasashe da dauloli. Ya yi amfani da iliminsa na tarihi ya ƙwato wa Uban ƙasa (Hakimi) na Jandutsi (gari ne a cikin Jega, jahar Kebbi) haƙƙinsa na kujerarsa da aka so a juya akalarta zuwa ga wani mutum daban. Saboda ya je har wurin Sarkin Gwandu[13] (wanda shi ne ke da ikon naɗa Uban ƙasar), ya tsaya a gabansa, kamar yadda lauya ke tsayawa a gaban alƙali. Ya bayar da tarihin yadda sarautar garin take, da kuma waɗanda suke gadonta tun kaka-da-kakanni. Sannan kuma, ya yi nasara a kan wannan fafatukar da ya yi ta amfani da ilmin tarihin da Allah ya ba shi. Haka kuma, an gayyace shi har Jamhuriyyar Nijar domin sanar da Zabarmawa tarhinsu dangane da shigowarsu Nijar.

A taƙaice, Muhammadu Sambo Wali fitaccen mutum ne musamman a ƙasashen Sakkwato, Kabi da kuma Zamfara. Haka kuma, malamin makaranta ne, marubuci waƙoƙin Hausa, sannan kuma masanin tarihi. Saboda irin ficen da ya yi a waɗannan ƙasashen ne ya sa ake jin sa a garuruwan da aka ambata. Da wahala a tambayi mutum musamman ma’abuci sauraron rediyo, ‘wane ne Sambo Wali?’ ya kasa bayar da amsar ko wane ne shi. Sannan zai yi wahala a je jami’o’i da kwalej-kwalej na Arewacin Nijeriya, musamman a sassan Nazarin Harsunan Nijeriya ko na Nazarin Harshen Hausa, a tambayi Sambo Wali a gaza bayar da bayani ko wane ne shi. Saboda an rubuta kundaye na neman takardar shaidar digiri na ɗaya da na biyu (B.A da M.A) da na neman takardar shaidar malanta (NCE) da kuma maƙalu na tarurrukan ƙara wa juna ilimi[14] a kan waƙoƙin wannan mashahurin marubucin waƙoƙin Hausa. Sannan kuma, ɗaliban tarihi da dama suna zuwa wurinsa domin neman ilimin tarihi. Ba ɗalibai masu neman digiri ko shaidar malanta kaɗai suka amfana da fasahar da Allah ya yi masa ba. Domin malamai ma masu koyarwa sun ƙaru, kuma suna ƙaruwa da baiwar da Allah ya yi masa. Saboda sun rurrubuta littattafai masu tsokaci a kan waƙoƙinsa. Inda suke bayyana ire-iren fasahohi da amfani da ilimin da waƙoƙin suka ƙunsa. Da kuma irin bayanin tarihin da suke samowa daga gare shi.

Ya bayar da gudummawa a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar Hausawa. Idan muka ɗauki harshe, za mu ga cewa, ya bayar da gudummawa wajen yaɗa shi da kuma raya shi. Saboda rubuta waƙoƙi a cikin harshe na ɗaya daga cikin abubuwa ko hanyoyin da ke rayar da harshe. Sannan kuma, ya bayar da gudummawa wajen haɓakawa da raya adabin Hausa. Domin waƙa babban lambu ce a adabin Hausa. Haka kuma, takan ƙara fito wa da ɗabi’un al’umma da yadda zamantakewarsu ya kamata ta kasance. Don haka, za a iya cewa, ya taka rawa wajen daidaita zamantakewar al’ummar Hausawa. Sannan kuma, ya bayar da gudummawa wajen taimaka wa Hausawa da ma waɗanda ba su ba, sanin tarihin wani abu wanda ya shafi ƙasashensu da al’adunsu da kuma zamantakewarsu a da.

A ƙarshe, Sambo Wali yana da aure, wanda ya fara yi a shekarar 1964. A halin yanzu yana da mata biyu (Hauwa’u da Lubabatu). Daga lokacin da ya yi aure zuwa yau, Allah ya albarkace shi da samun ‘ya’ya maza da mata. Ga dai jerin ‘ya’yansa, kamar haka:

‘Ya’ya Maza

1.     Dakta Abduljalil (Alhaji)

2.     Ibrahim Khalil (ya rasu)

3.     Abubakar Sadiƙ (ya rasu)

4.     Junaidu (Nakuci)

5.     Muhammadu Bello

6.     Barrister Muhammadu Lema

7.     Dakta Muhammadu Mustapha

8.     Ja’afarus Sadiƙ

9.     Harun Arrashid

‘Ya’ya Mata

10. A’ishatu (ɗiyar ‘Yan Mamma)

11. Asma’u  (Jamila)

12. Labratu

13. Hajaru

14. Khadijatu

15. Fatimatu

16. Zainabu

17. Ruƙayyatu

18. Hafsatu

19. Halimatus Sa’adiyya (ta rasu).

Duka-duka, Allah ya bai wa Muhammadu Sambo Wali ‘ya’ya goma sha tara ne, sai dai akwai huɗu (Ibrahim, Abubakar, Labratu, Halimatus Sa’adiyya[15]) waɗanda suka rasu. Yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar ne a raye.

Mallam Sambo Wali ya rasu ranar Talata 24 ga watan Yuni, 2025 miladiyya wanda ya yi daidai da 29 ga watan Zul-Hijja 1446 hijiriyya, bayan kwashe kimanin shekaru goma yana jinya. Duk da wannan jinya da ya yi da kuma yanayi na tsufa, Allah bai sa hankalinsa da tunaninsa sun gushe ba. A cikin wannan yanayin na tsufa da jinya mutane sukan je wurinsa domin neman tarihi da tuna musu abubuwa da dama da su kansu sun kasa tunawa.

An yi jana'izarsa a cikin gidan Sarkin Musulmi, aka kuma turbuɗe shi a Hubbaren Shehu Usmanu dan Fodiyo cikin garin Sakkwato.

Da fatar Allah ya saka masa da alheri, ya gafarta masa, ya sa aljanna ce makomarsa. Amin[16].


Wasu daga cikin Ayyukan Mallam Muhammadu Sambo Wali

Waƙoƙinsa Na Ƙarni Na Ashirin (Ƙ. 20)

1. Waƙoƙin Addini

·       Tauhidi Nazari

·       Roƙon Allah

·       Yabon Annabi (SAW)

·       Addu’a

2. Waƙoƙin Tarihi

·       Tarihin Hijirar Shehu Da Kafa Daular Usmaniyya

·       Waƙar L.G.R. 1975

3. Waƙoƙin Wayar Da Kai

·       Waƙar IFAD

·       Amfanin Shukka Itace (bishiyoyi)

·       Gasar Noma

·       Tahamisin ‘Gona da Mallan’

·       Lafiya Uwar Jiki

·       Matakan Kirkin Jiharmu

·       Na Fara Kiran Ku ‘Yan Yara


4. Waƙoƙin Gargaɗi

·       Gargaɗi

·       Gargaɗi Kan Gurgusowar Hamada Da Zaizayar Ƙasa

·       Gaskiya Mugunyar Magana

·       To Da Ke Nike

·       Shaye-Shaye Aibi Na


5. Waƙoƙin Faɗakarwa

·       Ku Bar Zaman Banza Da Barace-Barace

·       Shirin Zamani (Tahamisi)

·       Kishin Ƙasa

·       Yaƙi da Jahilci


6. Waƙoƙin Siyasa

·       Gidauniyar Jihar Sakkwato


7. Waƙoƙin Yabo

·       Jamborodo (Tahamisi)


8. Waƙoƙin Soyayya

·        ‘Yarkiɗi


9. Waƙoƙin Talla

·       Waƙar Omo

·       Waƙar King Cola

·       Kamfanin Westek

·       Kamfanin Haji Yaro Boɗinga

10. Waƙoƙin Nishaɗi

·       Naira Alfarmar Zamani


11.  Sauran Waƙoƙi

·       Tsangwama da Gunaguni

·       Ƙalubale Ga Masu Sukar Shan Taba-gari

 

Waƙoƙinsa Na Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙ. 21) 

1. Waƙoƙin Tarihi

·       Tarihin Masarautar Gwandu Ta Gidan Hassan Ɗan Abdullahi

·       Bin Shari’a Da Adalci Su Ne Kayan Adon Masarautar Gwandu

·       Tarihin Zabarmawa Da Ƙasarsu Ta Asali Da Sunan Kakansu

·       Gudummuwar San’inna Gari-Hanaye Ga Jihadin Shehu

·       Tunawa Da Ayyukan Maimartaba Sarkin Argungu Muhammadu Mera


2. Waƙoƙin Wayar Da Kai

·       Shan’inna (Polio)

·       Bunƙasa Ayyukan Noman Fadama

·       Kula da Lafiyar Mata Da Ƙananan Yara

·       Cika Alƙawali Aikinka Na


3. Waƙoƙin Faɗakarwa

·       Mu Jajirce Ga Aikin Gayya

·       Ku Tashi Da Himma Maza Zuwa Aikin Gayya

·       Zaman Lafiya


4. Waƙoƙin Siyasa

·       Ranar ‘Yancin Nijeriya

·       Taya Sarkin Yamma Aliyu Magatakarda Wamakko Murnar Zama Gwamnan Sakkwato

·       Albishirin Matafiya Gwamnatin Sarkin Yamman Daular Usmaniyya

·       Nasarorin Aliyu Magatakarda Wamakko

·       Ba A Taɓin Maza Su Koma Su Yi Kwance

·       Ga Ƙasa Samun Abin Ƙwarai Dace Na


5. Waƙoƙin Yabo

·       Du’a’i Ga Mai’alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na’ukku

·       ‘Zauren Waƙa’ Muhimmi Na

·       Manufofin Hassan Kangiwa

 

 

Rubuce-Rubucen Mallam Muhammadu Sambo Wali Na Tarihi

 

1. Shigowar Fulani Ƙasar Hausa Da Kyakkyawar Zamantakewarsu Da Haɓe

2. Gobirawa Da Asalinsu

3. Tarihin Gimbanawa

Taƙaitaccen Tarihin Masarautar Jega

Taƙaitaccen Tarihin Mallam Abdussalami Bagimbane

Wasiccin Jada Maijega

Tarihin Gidan Mujahidu ɗan Abdussalam

Tarihin Dangantakar Dagelawa da Sambawa da Gimbanawa

4. Asalin Hausawa Ga Tarihi

5. Tushen Arawa Tun Daga Abuyazid (Bayajida)

6. Asalin Kanta Ɗan Makata Ɗan Kotai       

8. Tarihin Sissilɓe (Sulluɓawa)

9. Tarihin Ƙasar Yauri A Taƙaice

10. Faɗakarwa A Kan Haɗin Kan Musulmi Da Matsayin Bara Da Raraka A Musulunci



[1] Ta dalilinsa da jama’arsa ne aka fara jihadin jaddada addinin Musulunci a ƙasar Hausa. Duba ‘Tarihin Abdussalami Bagimbane’ na Muhammadu Sambo Wali.

[2] Saboda birnin Alƙalawa asalinsa na Gimbanawa ne. Gobirawa suka yi musu zamba-cikin-aminci suka ƙwace birnin. Wato bayan sun ɗauki lokaci mai tsawo a ƙasar Agadez, Attawariƙ (Buzaye) na kashe musu sarakuna har kusan guda hamsin, sai suka gudo suka yo birnin Kunya (yana cikin Damagaram, Nijar yanzu), inda Sarkin Borno Mai Ari ya ba su mafaka. Daga nan kuma suka yo ƙasar Hausa, inda Sarkin Zamfara ya ba su mafaka cikin birnin Lalle (yana cikin Madawa, Nijar yanzu) kusa ga birnin Alƙalawa. To, daga nan ne bayan sun saki jiki, sai suka yi ta yunƙurin cin birnin da yaƙi kimanin shekaru goma shatakwas, amma ba su sami nasara ba. Suka yanke shawarar yin amana da Gimbanawa. Bayan an yi amanar, sai suka yi zamba-cikin-aminci, suka auka wa birnin a daidai lokacin da Gimbanawa suke gona, suna noma. Suka ƙwace birnin ba tare da wata wahala ba. Duba ‘Tarihin Gobirawa Da Asalinsu’ na Sambo Wali, domin ƙarin bayani.

[3] Shi ne waziri na shida a tsarin wazirran Sakkwato. Ya yi wazircin daga 1910 zuwa 1912 miladiyya.

[4] Shi ne waziri na farko a Sakkwato bayan Shehu Abdullahi ɗan Fodiyo ya koma Gwandu. Ya yi wazirci daga 1817 zuwa 1842. Ya rasu a shekarar 1850 miladiyya. Duba Jean Boyd da Beverly B. Mack The Collected Works of Nana Asma’u: Daughter of Usman ɗan Fodiyo (1793 – 1864)  (1999;  Nigerian Publishing) shafi na 228.

[5] Futa-Toro na cikin ƙasar Senegal a Afurka Ta Yamma.

[6] D.O (District Officer) wato Jami’in  Gunduma.

[7] Cikakken sunansa shi ne Mr. Neil Skinner. Baturen Ingila ne ɗan Mulkin Mallaka. Shi ne ya rubuta Kamus Na Turanci Da Hausa (English – Hausa Illustrated Dictionary): Babban Ja-gora ga Turanci (1965).

[8] National Broadcasting Corporation.

[9] Sabon sunan da aka sa wa gidan rediyon ke nan a 1979. Kuma Sambo Wali ne ya ba shi wannan suna bisa ga dalilan cewa, birnin Zamfara yana bisa ga Gulbin Rima. Alƙalawa birnin Gobirawa yana bisa ga Gulbin Rima. Sakkwato da Wurno manyan biranen Daular Usmaniyya suna bisa ga Gulbin Rima. Gungu da Surame manyan biranen Kanta suna bisa ga Gulbin Rima. Birnin Kabi da Argungu biranen sarautar Kabawa kashi na biyu, suna bisa ga Gulbin Rima.

[10] Centre for Islamic Studies, UDU, Sokoto.

[11] Lokacin da tsufa ya kama shi da kuma rashin isasshiyar lafiya.

[12] Wadda ya yi a 1951, wato yana da shekaru 14.

[13] Alhaji Iliyasu Bashar.

[14] Ni kaina na rubuta guda biyu na haɗaka. Ɗaya a cikin harshen Hausa, ɗaya kuma a cikin harshen Ingilishi. Ga sunayensu kamar haka:

1.      ‘Muhammadu Sambo Wali (Basakkwace): Gudummawarsa Ga Ci Gaban Adabi Da Tarihi’. Maƙalar da aka gabatar a Taron Ƙasa-da-Ƙasa na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci da ke Jami’ar Bayero, Kano game da ‘Matsayin Fasaha ga Ci Gaba’ [The Role of Art to Development]. (Sambo, A.W. da Alfanda, A.A. 

2 ‘The Role of Hausa Written Poets in Conflict Resolution: A Case Study of Sambo Wali Giɗaɗawa’ [Rawar da Marubuta Waƙoƙin Hausa ke takawa wajen samar da Zaman Lafiya: Nazarin a kan Sambo Wali Giɗaɗawa]. Maƙalar da aka gabatar a taro na 31 na Ƙungiyar Manazarta Kimiyyar Harshe ta Nijeriya (Linguistic Association of Nigeria) a Jami’ar Ilimi ta Ignatius Ajuru da ke birnin Fatakwal, jihar Rivers. (Ahmad, A.A. da Sambo, A.W. 2017). 

[15] Ta rasu ranar 17 ga Okotoba, 2016.

[16] Dakta Almustapha (Mujtaba) Sambo Wali ya rubuta wannan tarihi tare da taimakon mahaifinsa Sambo Wali a ranar Alhamis 11 ga Agusta, 2016 Miladiyya, daidai da 8 ga Zulƙi’ida, 1437 Hijiriyya. An sabunta wannan tarihi bayan rasuwarsa a ranar Assabar 29 ga Yuni, 2025 Miladiyya, daidai da 3 ga Muharram, 1447 Hijiriyya.



A Brief Biography of a Philanthropist, Mallam Muhammadu Sambo Wali

 

 


Brief Biography of Mallam Muhammadu Sambo Wali

(a School Teacher, a Journalist, a Researcher, a Historian, and a Hausa Poet)

By

ALMUSTAPHA SAMBO WALI, PhD.

Muhammadu Sambo Wali was born in Sokoto city on Friday, July 9, 1937, which corresponds to Rabi'u-Thani 30, 1356 AH. His father's name was Muhammadu Salisu, and his mother's name was A'ishatu. He was of Gimbanawa descent on his father's lineage and Fulani on his mother's side. He grew up in a household known for the importance of education and history, especially knowledge of lineage and ancestry. He was the son of Muhammadu Salisu, who was the son of Malam Yahya. Malam Yahaya was the son of Ahmadu, popularly known as Ladan Ɗanhajara. Ahmadu was the son of Alkali of Zamfara, Muhammadu. Muhammadu was the son of Malam Abdussalami Bagimbane[1] (a disciple of Shehu Usmanu Ɗanfodiyo). Abdussalami was the son of Malam Ibrahim. Malam Ibrahim was the son of Malam Shaharu (also known as Mallam Jaɓɓo Maigida Marannu). Malam Shaharu was the son of Mallam Hammadi Mai Babban Burgami, through whom the Gobirawa conquered Alkalawa city[2].

On his mother's lineage, he was Fulani, as previously stated. His mother, A'ishatu, was the daughter of Marafan Wazirin Sokoto, Mallam Buhari, popularly known as Marafa Tsoho. Marafa Tsoho was the son of Waziri Sambo[3] (Ambo). Waziri Sambo was the son of Ɗangaladima Ahmadu. Ɗangaladima Ahmadu was the son of Waziri Usman Giɗaɗo[4] (a disciple and son-in-law of Shehu) and Nana Asma'u. Waziri Giɗaɗo was the son of Lema. Nana Asma'u was the daughter of Shehu Usman. Usman was the son of Fodiyo. Fodiyo was the son of Usmanu. Usmanu was the son of Salihu. Salihu was the son of Haruna. Haruna was the son of Muhammadu Gurɗo. Muhammadu Gurɗo was the son of Jaɓɓo. Jaɓɓo was the son of Sambo. Sambo was the son of Buba Baba. Buba Baba was the son of Baba Masarana. Baba Masarana was the son of Ayyuba. Ayyuba was the son of Musa Jakollo. Musa Jakollo was from Futa-Toro[5].

Sambo Wali received his early education from his father. As he narrated:

"When I was about six years old, my father voluntarily retired from his judicial work. It wasn't because he was asked to leave. When I was about ten years old, a young District Officer (D.O.)[6] in Sokoto named Mr. Skinner[7] employed my father for historical research tours and paid him a salary. My father also taught him Hausa. During this time, my father always traveled with me because my mother had passed away. Wherever they went, I went with them. Therefore, I studied the Quran and the books of Lahallari and Ishimawi with my father. In short, my father taught me Roman script writing and arithmetic. It wasn't until 1955, when I was 18 years old, that he stopped traveling with me, and I settled in Sokoto."

Sambo Wali continued his religious studies with other teachers such as Malam Yahya Nawawi, Alkalin Lardi, Malam Joɗi, Malam Maigandi Giɗaɗawa, Malam Babi Unguwar Dutsin Assada, Malam Sagware of Unguwar Alkanci, Malam Shayau of Kuci town, and Waziri Junaidu, all within present-day Sokoto State. He often recalled the advice these teachers gave him and affirmed that they provided him with an excellent upbringing. May Allah reward them with goodness and grant them His mercy.


Formal Education and Career

Regarding his formal education, he was not left behind. He started primary school at 'Waziri Ward' school in 1945. In 1963, the 'Arabic Teachers' College,' now known as 'Abubakar Gummi Memorial Secondary School,' was opened, and he was among its students. There, he obtained a Grade III certificate. Later, he also obtained a Grade II certificate from the same school. From there, he went to the 'School for Arabic Studies' in Kano, where he undertook a vocational course.

Sambo Wali began his teaching career at 'Government Craft School' in Sokoto on September 15, 1959. He continued teaching in various schools until 1978. In that year, the Federal Government requested him to switch from teaching to journalism in the National Broadcasting Corporation (NBC)[8] in Sokoto. He accepted the government's call and began working at the Federal Radio Corporation, Sokoto State chapter (Rima Radio[9]), from 1978 until 1985. He served as the head of the radio's religious affairs department.


Contributions to Research and Public Awareness

His intelligence and diligence led the then Vice-Chancellor of Usmanu Danfodiyo University, Sokoto, late Professor Mahadi Adamu Ngaski, to invite him to work at the university. He accepted, leaving journalism to return to his former profession of teaching and research. He started working at the university in 1985 at the Centre for Islamic Studies[10] until 1996 as a researcher and lecturer in Islamic studies. After this period, he retired from government service. However, Rima Radio again requested him to work for them on a part-time basis, specifically on an awareness program called 'Zauren Mai Anguwa.' This program continued with his involvement from 1996 until 2015[11]. In this program, he was affectionately called 'Mallam Maiƙunƙuwa.'

Sambo Wali served as a representative for various government bodies and organizations for national, community, and language development. He was a member of the Sokoto State Traditional Culture Promotion Committee established by the state government under the Sokoto State Ministry of Traditional Culture in 1976. He also served as one of the representatives appointed by the Sokoto State government to the committee for providing accommodation for Almajiris and disabled individuals in 1979. He was a member of the National Association of Hausa Poets and Literary Scholars and also served as its Sokoto State chairman. He achieved significant success in Hausa poetry competitions and received numerous awards for public enlightenment at state, national, and non-governmental levels.


Poetic and Historical Prowess

Allah blessed Sambo Wali with the gift of writing, particularly artistic and wise writing. He wrote and recited Hausa poems (and also Fulani ones). Furthermore, he wrote extensively on history, especially that of the Sokoto Caliphate and its lineages, and shared this knowledge with the public. He started composing poetry at the age of eleven. His first poem was about the 'bullying and gossip' he experienced from his childhood playmates because he was with them, but they were not his peers. However, he did not name the poem, and it lacked a consistent meter or rhyme. His second poem was 'Challenge to Critics of Chewing Tobacco (Taba-gari)'[12], addressing the strict prohibition of chewing tobacco (which is placed under the lip) by some people. In the poem, he described his encounters with some individuals, especially those from Wazifan Jega and Ƙauran-Namoda.

Quantifying the poems of any poet or songwriter is extremely difficult. Even the poets themselves can hardly specify all the poems they composed in their lifetime; it's usually an estimation. Therefore, Sambo Wali himself did not know the exact number of poems he wrote. He confirmed that he wrote many poems on various aspects of community life. The poems he wrote most frequently were those aimed at raising public awareness about ongoing issues. He also wrote poems of praise, advice, sermons, politics, warnings, expressions of desire, and advertisements. State or federal governments or non-governmental organizations would often request Muhammadu Sambo Wali to write a poem for them (and recite it on media outlets or at gatherings) on any resolution or policy they wished to convey to the public.

Sambo Wali did not stop at poetry alone. He was also a historian, particularly of the Sokoto Caliphate and the kingdoms of Kebbi and Gobir. He wrote numerous historical works concerning these kingdoms and empires. He used his historical knowledge to reclaim the right of the District Head (Hakimi) of Jandutsi (a town in Jega, Kebbi State) to his chieftaincy, which was almost diverted to another person. He went before the Emir of Gwandu[13] (who had the authority to appoint the District Head) and stood before him like a lawyer before a judge. He presented the history of the chieftaincy of the town and those who inherited it from their ancestors. He succeeded in this struggle by using the historical knowledge that Allah had bestowed upon him. He was also invited to the Republic of Niger to inform the Zarmas about their history concerning their arrival in Niger.


Legacy and Influence

In summary, Muhammadu Sambo Wali was a prominent figure, especially in Sokoto, Kebbi, and Zamfara. He was also a school teacher, a Hausa poet, and a historian. His prominence in these regions made him well-known. It would be difficult to ask someone, especially a radio listener, "Who is Sambo Wali?" and for them not to know. Similarly, it would be hard to go to universities and colleges in Northern Nigeria, especially in departments of Nigerian Languages or Hausa Language Studies, and ask about Sambo Wali without receiving an explanation of who he was. This is because numerous undergraduate and postgraduate theses (B.A and M.A.), NCE projects, and conference papers[14] have been written about the poems of this renowned Hausa poet. Furthermore, many history students sought his knowledge of history. It was not only degree or NCE students who benefited from his God-given talent, but also the teaching staff who learned and continue to learn from his gift. They have written books commenting on his poems, highlighting the artistic techniques and knowledge contained within them, and the historical information they gleaned from him.

He contributed to various aspects of Hausa community life. In terms of language, he contributed to its spread and revitalization, as writing poetry in a language is one of the ways to keep it alive. He also contributed to the development and revitalization of Hausa literature, as poetry is a significant genre in Hausa literature. It also highlights community customs and how their social life should be. Therefore, it can be said that he played a role in stabilizing the social life of the Hausa community. He also helped Hausa people, and even non-Hausa speakers, understand the history of Hausa lands, cultures, and past social interactions.


Family and Passing

Finally, Sambo Wali was married, starting his first marriage in 1964. Before his demise, he had two wives (Hauwa'u and Lubabatu). From the time he got married until his passing, Allah blessed him with both male and female children. Here is a list of his children:

Male Children:

1.     Dr. Abduljalil (Alhaji)

2.     Ibrahim Khalil (deceased)

3.     Abubakar Sadiƙ (deceased)

4.     Junaidu (Nakuci)

5.     Muhammadu Bello

6.     Barrister Muhammadu Lema

7.     Dr. Muhammadu Mustapha

8.     Ja’afarus Sadiƙ

9.     Harun Arrashid

Female Children:

10. A’ishatu (diyar ‘Yan Mamma)

11. Asma’u (Jamila)

12. Labratu (deceased)

13. Hajaru

14. Khadijatu

15. Fatimatu

16. Zainabu

17. Ruƙayyatu

18. Hafsatu

19. Halimatus Sa’adiyya (deceased).

 

In total, Allah blessed Muhammadu Sambo Wali with nineteen children, but four (Ibrahim, Abubakar, Labratu, Halimatus Sa'adiyya[15]) have passed away. Fifteen of his children are currently alive.


Demise

Mallam Sambo Wali passed away on Tuesday, June 24, 2025, corresponding to Dhul-Hijjah 29, 1446 AH, after battling an illness for approximately ten years. Despite the illness and old age, Allah did not allow his intellect and memory to diminish. Even in this state of old age and illness, people would visit him to seek historical knowledge and for him to recall many things they could not remember. He was buried in 'Hubbaren' Shehu Usmanu dan Fodiyo (a graveyard where Shehu Usmanu was buried).

May Allah reward him with goodness, forgive him, and make Paradise his final abode. Amen[16].


Some Works of Mallam Muhammadu Sambo Wali

20th Century Poems (20th C.)

1. Religious Poems

●      Tauhidi Nazari (Describing Oneness of Allah)

●      Roƙon Allah (Plea to Allah)

●      Yabon Annabi (SAW) (Praise of the Prophet SAW)

●      Addu’a (Prayer)

2. Historical Poems

●      Tarihin Hijirar Shehu Da Kafa Daular Usmaniyya (History of Shehu's Migration and the Establishment of the Sokoto Caliphate)

●      Waƙar L.G.R. 1975 (L.G.R. Song 1975)

3. Awareness Poems

●      Waƙar IFAD (IFAD Song)

●      Amfanin Shukka Itace (bishiyoyi) (The Benefit of Planting Trees)

●      Gasar Noma (Farming Competition Song)

●      Tahamisin ‘Gona da Mallan’ (Takhmis of 'Farm and Scholar' Song)

●      Lafiya Uwar Jiki (The Benefits of Health)

●      Matakan Kirkin Jiharmu (The Virtue of Our State)

●      Na Fara Kiran Ku ‘Yan Yara (O Children, Be Good Ones)

4. Warning Poems

●      Gargaɗi (Warning)

●      Gargaɗi Kan Gurgusowar Hamada Da Zaizayar Ƙasa (Warning on Desertification and Soil Erosion)

●      Gaskiya Mugunyar Magana (Truth is Bitter)

●      To Da Ke Nike (It's All About You)

●      Shaye-Shaye Aibi Na (Addiction is a Flaw)

5. Enlightenment Poems

●      Ku Bar Zaman Banza Da Barace-Barace (Stop Idleness and Begging)

●      Shirin Zamani (Tahamisi) (Modern Preparation (Takhmisi))

●      Kishin Ƙasa (Nationalism)

●      Yaƙi da Jahilci (War on Ignorance)

6. Political Poems

●      Gidauniyar Jihar Sakkwato (Sokoto State Foundation)

7. Praise Poems

●      Jamborodo (Takhmisi)

8. Love Poems

●      ‘Yarkiɗi

9. Advertisement Poems

●      Waƙar Omo (Omo Song)

●      Waƙar King Cola (King Cola Song)

●      Kamfanin Westek (Westek Company)

●      Kamfanin Haji Yaro Boɗinga (Haji Yaro Boɗinga Company)

10. Entertainment Poems

●      Naira Alfarmar Zamani (Naira, The Privilege of the Era)

11. Other Poems

●      Tsangwama da Gunaguni (Bullying and Grumbling)

●      Ƙalubale Ga Masu Sukar Shan Taba-gari (Challenge to Critics of Chewing Tobacco)


21st Century Poems (21st C.)

1. Historical Poems

●      Tarihin Masarautar Gwandu Ta Gidan Hassan Ɗan Abdullahi (History of Gwandu Emirate of the House of Hassan Ɗan Abdullahi)

●      Bin Shari’a Da Adalci Su Ne Kayan Adon Masarautar Gwandu (Adhering to Sharia and Justice are the Ornaments of Gwandu Emirate)

●      Tarihin Zabarmawa Da Ƙasarsu Ta Asali Da Sunan Kakansu (History of the Zarmas, Their Original Land, and Their Ancestor's Name)

●      Gudummuwar San’inna Gari-Hanaye Ga Jihadin Shehu (Contribution of San’inna Gari-Hanaye to Shehu's Jihad)

●      Tunawa Da Ayyukan Maimartaba Sarkin Argungu Muhammadu Mera (Remembering the Deeds of His Royal Highness Emir of Argungu Muhammadu Mera)

2. Awareness Poems

●      Shan’inna (Polio)

●      Bunƙasa Ayyukan Noman Fadama (Boosting Fadama Farming Activities)

●      Kula da Lafiyar Mata Da Ƙananan Yara (Care for the Health of Women and Young Children)

●      Cika Alƙawali Aikinka Na (Fulfilling Promises is Your Habit)

3. Enlightenment Poems

●      Mu Jajirce Ga Aikin Gayya (Let Us Persevere in Communal Work)

●      Ku Tashi Da Himma Maza Zuwa Aikin Gayya (Rise with Zeal, Men, Towards Communal Work)

●      Zaman Lafiya (Peace)

4. Political Poems

●      Ranar ‘Yancin Nijeriya (Nigeria's Independence Day)

●      Taya Sarkin Yamma Aliyu Magatakarda Wamakko Murnar Zama Gwamnan Sakkwato (Congratulating Sarkin Yamma Aliyu Magatakarda Wamakko on Becoming Governor of Sokoto)

●      Albishirin Matafiya Gwamnatin Sarkin Yamman Daular Usmaniyya (Good News for the Fellows of the Government of the Sarkin Yamma of the Caliphate)

●      Nasarorin Aliyu Magatakarda Wamakko (Achievements of Aliyu Magatakarda Wamakko)

●      Ba A Taɓin Maza Su Koma Su Yi Kwance (Men Don't Back Down and Lie Down)

●      Ga Ƙasa Samun Abin Ƙwarai Dace Na ta Aminu Waziri Tambuwal (For the Land to Gain Something Good is Fortunate, Song for Aminu Waziri Tambuwal)

5. Praise Poems

●      Du’a’i Ga Mai’alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na’ukku (Prayer for His Eminence, The Sultan of Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar III)

●      ‘Zauren Waƙa’ Muhimmi Na (The Journal Zauren Waƙa is Important)

●      Manufofin Hassan Kangiwa (Good Intention of Hassan Kangiwa)


Historical Writings of Mallam Muhammadu Sambo Wali

1.     Shigowar Fulani Ƙasar Hausa Da Kyakkyawar Zamantakewarsu Da Haɓe (The Arrival of Fulani in Hausa Land and Their Good Relationship with the Hausa)

2.     Gobirawa Da Asalinsu (The Gobirawa and Their Origin)

3.     Tarihin Gimbanawa (History of the Gimbanawa)

○      Taƙaitaccen Tarihin Masarautar Jega (Brief History of Jega Emirate)

○      Taƙaitaccen Tarihin Mallam Abdussalami Bagimbane (Brief History of Mallam Abdussalami Bagimbane)

○      Wasiccin Jada Maijega (The Will of Jada Maijega)

○      Tarihin Gidan Mujahidu ɗan Abdussalam (History of the House of Mujahidu son of Abdussalam)

○      Tarihin Dangantakar Dagelawa da Sambawa da Gimbanawa (History of the Relationship between Dagelawa, Sambawa, and Gimbanawa)

4.     Asalin Hausawa Ga Tarihi (The Origin of Hausa People in History)

5.     Tushen Arawa Tun Daga Abuyazid (Bayajida) (The Origin of the Arawa from Abuyazid (Bayajida))

6.     Asalin Kanta Ɗan Makata Ɗan Kotai (The Origin of Kanta son of Makata son of Kotai)

7.     Tarihin Sissilɓe (Sulluɓawa) (History of the Sissilɓe (Sulluɓawa))

8.     Tarihin Ƙasar Yauri A Taƙaice (A Brief History of Yauri Land)

9.     Faɗakarwa A Kan Haɗin Kan Musulmi Da Matsayin Bara Da Raraka A Musulunci (Awareness on Muslim Unity and the Status of Begging and Loafing in Islam)


Footnotes

[1] Through him and his community, the jihad for the revival of Islam in Hausaland began. See 'Tarihin Abdussalami Bagimbane' by Muhammadu Sambo Wali.

[2] Because the city of Alkalawa originally belonged to the Gimbanawa. The Gobirawa deceived them and seized the city. This happened after they spent a long time in Agadez, where the Tuaregs (Buzaye) killed almost fifty of their rulers, so they fled to Kunya (now in Damagaram, Niger), where Sarkin Borno Mai Ari granted them refuge. From there, they came to Hausaland, where Sarkin Zamfara granted them refuge in Lalle city (now in Madawa, Niger), near Alkalawa city. It was from there that, after settling in, they attempted to conquer the city by war for about eighteen years, but did not succeed. They decided to make peace with the Gimbanawa. After the peace treaty, they cunningly attacked the city at the very time the Gimbanawa were in their farms, cultivating. They seized the city without any difficulty. See 'Tarihin Gobirawa Da Asalinsu' by Sambo Wali for more details.

[3] He was the sixth vizier in the line of Sokoto viziers. He served as vizier from 1910 to 1912 AD.

[4] He was the first vizier in Sokoto after Shehu Abdullahi ɗan Fodiyo moved to Gwandu. He served as vizier from 1817 to 1842. He died in 1850 AD. See Jean Boyd and Beverly B. Mack, The Collected Works of Nana Asma’u: Daughter of Usman ɗan Fodiyo (1793 – 1864) (1999; Nigerian Publishing), page 228.

[5] Futa-Toro is in Senegal, West Africa.

[6] D.O. (District Officer).

[7] His full name was Mr. Neil Skinner. He was a British colonial officer. He wrote the English–Hausa Illustrated Dictionary: A Great Guide to English (1965).

[8] National Broadcasting Corporation.

[9] This is the new name given to the radio station in 1979. Sambo Wali gave it this name because Sokoto city is on the Rima River. Alkalawa, the city of the Gobirawa, is on the Rima River. Sokoto and Wurno, the major cities of the then Sokoto Caliphate, are on the Rima River. Gungu and Surame, the major cities of Kanta, are on the Rima River. Kebbi city and Argungu, the cities of the second phase of Kebbi chieftaincy, are on the Rima River.

[10] Centre for Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

[11] At the time, he became old and had insufficient health.

[12] Which he composed in 1951, when he was 14 years old.

[13] Alhaji Iliyasu Bashar.

[14] I co-authored two papers. One in Hausa, and one in English. Their titles are as follows:

1.     'Muhammadu Sambo Wali (Basakkwace): Gudummawarsa Ga Ci Gaban Adabi Da Tarihi' (Muhammadu Sambo Wali (Basakkwace): His Contribution to the Development of Literature and History). A paper presented at the International Conference of the Faculty of Arts and Islamic Studies at Bayero University, Kano, on 'The Role of Art to Development'. (Sambo, A.W. & Alfanda, A.A. 2016).

2.     'The Role of Hausa Written Poets in Conflict Resolution: A Case Study of Sambo Wali Giɗaɗawa'. A paper presented at the 31st conference of the Linguistic Association of Nigeria at Ignatius Ajuru University of Education, Port Harcourt, Rivers State. (Ahmad, A.A. & Sambo, A.W. 2017).

[15] She died on October 17, 2016.

[16] Dr. Almustapha (Mujtaba) Sambo Wali wrote this history with the help of his father, Sambo Wali, on Thursday, August 11, 2016 AD, corresponding to Dhul-Qi'dah 8, 1437 AH. This history was updated on Saturday, June 29, 2025 AD, corresponding to Muharram 3, 1447 AH, after Sambo Wali’s death.

CALL FOR PAPERS_ JOLAN SUPPLEMENT IN HONOUR OF PROFESSOR ISMA'IL JUNAIDU

                                                                                             


CALL FOR SUBMISSION OF PAPERS: JOLAN SUPPLEMENT IN HONOUR OF PROFESSOR ISMA'IL JUNAIDU


Esteemed colleagues,


The Linguistic Association of Nigeria (LAN) cordially invites participants from CLAN-AUK 2024 and other linguists to submit revised or new papers for publication in a special JOLAN Supplement dedicated to the late Professor Isma'il Junaidu, former Executive Director of the National Educational Research and Development Council (NERDC).


Please review and adhere to the JOLAN Author's Guidelines here before submission.  Submissions not conforming to these guidelines will be rejected.


NB: Submissions should be sent to jolansupplement4junaidu@gmail.com and could be made in English or any Nigerian Language.


Key Dates:

  • Paper Submission: January 13, 2025 – March 13, 2025

  • Peer Review: March 17, 2025 – June 20, 2025

  • Publication: September 2025


For inquiries, please contact:

- Dr. A. S. Wali, Guest Editor (09050536762)