MUHAMMADU SAMBO WALI
(Malamin Makaranta, Masanin Tarihi, Marubuci Waƙoƙin Hausa)
daga
ALMUSTAPHA SAMBO WALI, PhD.
An haifi Muhammadu Sambo Wali a birnin Sakkwato, a ranar Jumu’a ta 9 ga watan Yuli, shekara ta 1937 Miladiyya. Wato daidai da 30 ga watan Rabi’u-Thani, shekara ta 1356 Hijiriyya. Sunan mahaifinsa shi ne Muhammadu Salisu. Mahaifiyarsa kuwa, sunanta A’ishatu. Bagimbane ne a wajen mahaifinsa. A wajen mahaifiyarsa kuwa Bafulatani ne. Ya rayu a gidan da aka san muhimmancin ilimi da tarihi musamman na sanin nasaba da salsala. Ɗa ne ga Muhammadu Salisu. Muhammadu Salisu ɗan Malam Yahya ne. Malam Yahaya ɗan Ahmadu ne, wanda aka fi sani da Ladan Ɗanhajara. Ahmadu ɗan Alƙalin Zamfara Muhammadu ne. Muhammadu ɗan Malam Abdussalami Bagimbane[1] (almajirin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo) ne. Shi kuwa Abdussalami ɗan Malam Ibrahim ne. Malam Ibrahim ɗan Malam Shaharu ne (wanda ake kira Mallam Jaɓɓo Maigida Marannu). Malam Shaharu ɗan Mallam Hammadi Mai Babban Burgami ne, wanda gare shi Gobirawa suka ci birnin Alƙalawa[2].
Ta ɓangaren mahaifiyarsa kuwa, Bafulatani ne kamar yadda bayani ya gabata. Sunan mahaifiyarsa A’ishatu ɗiyar Marafan Wazirin Sakkwato Mallam Buhari, wanda aka fi sani da Marafa Tsoho. Shi kuwa Marafa Tsoho ɗan Waziri Sambo[3] (Ambo) ne. Waziri Sambo ɗan Ɗangaladima Ahmadu ne. Ɗangaladima Ahmadu ɗan Waziri Usman Giɗaɗo[4] (almajirin Shehu) da Nana Asma’u ne. Waziri Giɗaɗo ɗan Lema ne. Ita kuwa Nana Asma’u ɗiyar Shehu Usman ce. Usman ɗan Fodiyo ne. Fodiyo ɗan Usmanu ne. Shi kuwa Usmanu ɗan Salihu ne. Salihu ko ɗan Haruna ne. Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ne. Muhammadu Gurɗo ɗan Jaɓɓo ne. Jaɓɓo kuma ɗan Sambo ne. Shi kuwa Sambo ɗan Buba Baba ne. Buba Baba ɗan Baba Masarana ne. Baba Masarana ɗan Ayyuba ne. Shi ko Ayyuba ɗan Musa Jakollo ne. Shi kuwa Musa Jakollo ya fito ne daga Futa-Toro[5].
Sambo Wali ya yi karatu ga mahaifinsa. Kamar yadda ya bayyana cewa:
“Ina da kusan shekara shidda mahaihina ya’ aje aikin shari’a bisa ra’ayin kainai. Ba don an ce masa ya bar aiki ba. Ina da kusan shekara goma wani ƙaramin di’o[6] na Sakkwato wanda ake kira Mista Skinner[7] ya ɗauki mahaihina aiki dangane da yawon binciken wuraren tarihi yana biyanai albashi. Kuma mahaihina yana koya masa Hausa. A wannan lokacin, ya kasance mahaihina yana tahiya tare da ni saboda dalilin mahaihiyata ta rasu. Ko’ina za su na tare da ni yaka tahiya. Saboda haka, ga mahaihina niy yi karatun Ƙur’ani da kuma littahwan Lahallari da Ishimawi. A taƙaice, mahaihina shi yak koya min rubutun boko da lissahi. Sai a shekara ta 1955, ina ɗan shekara 18, yab bay yawo da ni, niz zauna gida Sakkwato.”
Ya ci gaba da karatun addini daga wajen malamansa irin su Malam Yahya Nawawi, Alƙalin Lardi da Malam Joɗi da Malam Maigandi Giɗaɗawa da Malam Babi Unguwar Dutsin Assada da Malam Sagware na Unguwar Alkanci da Malam Shayau na garin Kuci da kuma Waziri Junaidu, duk a cikin jahar Sakkwato ta yau. A kowane lokaci yakan tuna ire-iren nasihohin da waɗannan malamai suka yi masa. Kuma ya tabbatar da cewa, sun ba shi kyakkyawar tarbiyya. Allah ya saka musu da alheri, ya jiƙansu da rahamarsa.
Ta fuskar karatun boko kuwa, ba a bar shi a baya ba. Ya fara karatun ilimantare (firamare) a makarantar ‘Waziri Ward’, a shekarar 1945 miladiyya. A 1963 aka buɗa makarantar ‘Arabic Teachers’ College’ wadda a yanzu aka sani da ‘Abubakar Gummi Memorial Secondary School’ tare da shi yana a matsayin ɗalibi. A nan ne ya sami takardar shaidar kammala karatu mai daraja ta uku (Grade III). Haka kuma, daga baya ya sami takardar kammala karatu mai daraja ta biyu (Grade II) a nan makarantar. Daga nan ya tafi makarantar koyon Larabci, wato ‘School for Arabic Studies’ da ke Kano, inda ya yi kwas na sanin makamar aiki.
Sambo Wali ya fara aikin koyarwa a ‘Government Craft School’ da ke Sakkwato, a ranar 15 ga watan Satumba, shekara ta 1959. Ya ci gaba da koyarwa a makarantu daban-daban har zuwa shekarar 1978 miladiyya. A cikin shekarar 1978 ne Gwamnatin Tarayya ta neme shi da ya sauya aikinsa na malamin makaranta zuwa aikin jarida a sashen yaɗa labarai na Tarayya (NBC)[8] da ke Sakkwato. A inda ya karɓi kiran hukuma ya kama aiki da Gidan Rediyon Tarayya sashen jahar Sakkwato (Rima Radio[9]), tun daga 1978 har zuwa 1985. Ya riƙi shugabancin sashen al'amurran addini na gidan rediyon.
Irin hazaƙa da ƙwazon da yake da shi ne ya sa Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (na wancan lokaci), Farfesa Mahadi Adamu Ngaski ya neme shi da ya zo jami’ar, ya yi musu aiki. Ya kuma yarda. Inda ya bar aikin jarida ya dawo wa tsohon aikinsa, wato koyarwa da kuma bincike. Ya fara aiki da jami’ar a 1985, a Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci[10] ta jami’ar har zuwa 1996 a matsayin mai bincike, wato ‘researcher’. Kuma mai koyar da darussan da suka shafi addinin Musulunci. Daga wannan lokaci kuma, sai ya ajiye aikin gwamnati. Sai dai kuma Gidan Rediyon Rima sun sake nemansa a kan ya riƙa yi musu aiki na wucen-gadi. Inda yake kama musu a wani shiri da suke yi na faɗakarwa mai suna ‘Zauren Mai Anguwa’. Tun daga wancan lokaci (1996) har zuwa 2015[11] ana aiwatar da wannan shirin tare da shi. Sannan kuma, akan kira shi ‘Mallam Maiƙunƙuwa’ a cikin wannan shirin.
Sambo Wali ya yi zama wakilin hukuma da ƙungiyoyi da dama na ci gaban ƙasa da al’umma da kuma harshe. Ya kasance cikin kwamitin yaɗa al’adun gargajiya na jahar Sakkwato wanda gwamnatin jaha ta kafa a ƙarƙashin ma’aikatar al’adun gargajiya ta jahar Sakkwato, a shekarar 1976. Haka kuma, ya taɓa kasancewa ɗaya daga cikin wakilan da gwamnatin jahar Sakkwato ta naɗa na kwamitin samar wa almajirai da musakai wurin zama a shekarar 1979. Yana cikin ƙungiyar marubuta da manazarta waƙoƙin Hausa ta ƙasa. Sannan kuma ya taɓa zama shugabanta na jahar Sakkwato. Ya yi ta samun nasara a gasannin da ake yi na marubuta waƙoƙin Hausa. Ya sami lambobin karramawa da dama a kan wayar da kan al'umma daga matakai na jaha da ƙasa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Allah ya yi wa Sambo Wali baiwa ta rubutu, kuma rubutu na fasaha da hikima. Domin yana rubuta waƙoƙin Hausa tare kuma da rera su (yana kuma rera na Fulatanci). Haka kuma, yana rubuta tarihi musamman na Daular Usmaniyya da dangoginta tare kuma da sanar da al’umma shi. Ya fara waƙa tun yana ɗan shekara goma shaɗaya. Waƙar da ya fara yi ita ce waƙar ‘tsangwama da gungunin’ da abokan kwanansa yara ke yi masa, saboda yana tare da su, amma kuma ba sa’anninsa ne ba. Sai dai bai yi wa waƙar suna ba. Kuma ba ta da wani tsayayyen kari ko amsa-amo. Waƙarsa ta biyu da ya rubuta, ita ce waƙar ‘Ƙalubale ga Masu Sukar Shan Taba-gari[12] a kan irin tsaurara haramcin shan taba-gari (wadda ake saƙalewa a leɓe) da wasu mutane suka yi. A waƙar, ya nuna irin yadda ya yi da wasu mutane musamman ‘yan wazifan Jega da na Ƙauran-Namoda.
Ƙididdige waƙoƙin kowane marubuci waƙoƙi ko kuma mawaƙi abu ne mai matuƙar wahala. Domin ko shi marubuci waƙoƙin ko mawaƙin da wahala ya iya ƙayyade waƙoƙin da ya yi a rayuwarsa, sai dai kawai a yi ƙirdado, wato a kimanta. Saboda haka, ko shi Sambo Wali bai san adadin yawan waƙoƙin da ya rubuta ba.Ya dai tabbatar da cewa, ya rubuta waƙoƙi da dama a kan fannoni rayuwar al’umma. Waƙoƙin da ya fi rubutawa su ne waɗanda suka shafi wayar da kan al’umma a kan wata matsala da take gudana. Haka kuma, ya rubuta waƙoƙin da suka shafi yabo da nasiha da wa’azi da siyasa da gargaɗi da sha’awa da kuma tallace-tallace. Gwamnatin jaha ko ta tarayya ko ƙungiyoyi masu zaman kansu kan nemi Muhammadu Sambo Wali ya rubuta musu waƙa (tare da rera ta a kafafen yaɗa labarai ko tarurruka) a kan duk wani ƙuduri ko manufar da suke son isarwa ga al’umma.
Sambo Wali bai tsaya a kan waƙoƙi kaɗai ba. Domin masanin tarihi ne, musamman tarihin da ya shafi Daular Usmaniyya da ƙasashen Kabi da Gobir. Saboda ya yi rubutun tarihi da dama wanɗanda suka shafi waɗannan ƙasashe da dauloli. Ya yi amfani da iliminsa na tarihi ya ƙwato wa Uban ƙasa (Hakimi) na Jandutsi (gari ne a cikin Jega, jahar Kebbi) haƙƙinsa na kujerarsa da aka so a juya akalarta zuwa ga wani mutum daban. Saboda ya je har wurin Sarkin Gwandu[13] (wanda shi ne ke da ikon naɗa Uban ƙasar), ya tsaya a gabansa, kamar yadda lauya ke tsayawa a gaban alƙali. Ya bayar da tarihin yadda sarautar garin take, da kuma waɗanda suke gadonta tun kaka-da-kakanni. Sannan kuma, ya yi nasara a kan wannan fafatukar da ya yi ta amfani da ilmin tarihin da Allah ya ba shi. Haka kuma, an gayyace shi har Jamhuriyyar Nijar domin sanar da Zabarmawa tarhinsu dangane da shigowarsu Nijar.
A taƙaice, Muhammadu Sambo Wali fitaccen mutum ne musamman a ƙasashen Sakkwato, Kabi da kuma Zamfara. Haka kuma, malamin makaranta ne, marubuci waƙoƙin Hausa, sannan kuma masanin tarihi. Saboda irin ficen da ya yi a waɗannan ƙasashen ne ya sa ake jin sa a garuruwan da aka ambata. Da wahala a tambayi mutum musamman ma’abuci sauraron rediyo, ‘wane ne Sambo Wali?’ ya kasa bayar da amsar ko wane ne shi. Sannan zai yi wahala a je jami’o’i da kwalej-kwalej na Arewacin Nijeriya, musamman a sassan Nazarin Harsunan Nijeriya ko na Nazarin Harshen Hausa, a tambayi Sambo Wali a gaza bayar da bayani ko wane ne shi. Saboda an rubuta kundaye na neman takardar shaidar digiri na ɗaya da na biyu (B.A da M.A) da na neman takardar shaidar malanta (NCE) da kuma maƙalu na tarurrukan ƙara wa juna ilimi[14] a kan waƙoƙin wannan mashahurin marubucin waƙoƙin Hausa. Sannan kuma, ɗaliban tarihi da dama suna zuwa wurinsa domin neman ilimin tarihi. Ba ɗalibai masu neman digiri ko shaidar malanta kaɗai suka amfana da fasahar da Allah ya yi masa ba. Domin malamai ma masu koyarwa sun ƙaru, kuma suna ƙaruwa da baiwar da Allah ya yi masa. Saboda sun rurrubuta littattafai masu tsokaci a kan waƙoƙinsa. Inda suke bayyana ire-iren fasahohi da amfani da ilimin da waƙoƙin suka ƙunsa. Da kuma irin bayanin tarihin da suke samowa daga gare shi.
Ya bayar da gudummawa a fannoni daban-daban na rayuwar al’ummar Hausawa. Idan muka ɗauki harshe, za mu ga cewa, ya bayar da gudummawa wajen yaɗa shi da kuma raya shi. Saboda rubuta waƙoƙi a cikin harshe na ɗaya daga cikin abubuwa ko hanyoyin da ke rayar da harshe. Sannan kuma, ya bayar da gudummawa wajen haɓakawa da raya adabin Hausa. Domin waƙa babban lambu ce a adabin Hausa. Haka kuma, takan ƙara fito wa da ɗabi’un al’umma da yadda zamantakewarsu ya kamata ta kasance. Don haka, za a iya cewa, ya taka rawa wajen daidaita zamantakewar al’ummar Hausawa. Sannan kuma, ya bayar da gudummawa wajen taimaka wa Hausawa da ma waɗanda ba su ba, sanin tarihin wani abu wanda ya shafi ƙasashensu da al’adunsu da kuma zamantakewarsu a da.
A ƙarshe, Sambo Wali yana da aure, wanda ya fara yi a shekarar 1964. A halin yanzu yana da mata biyu (Hauwa’u da Lubabatu). Daga lokacin da ya yi aure zuwa yau, Allah ya albarkace shi da samun ‘ya’ya maza da mata. Ga dai jerin ‘ya’yansa, kamar haka:
‘Ya’ya Maza
1. Dakta Abduljalil (Alhaji)
2. Ibrahim Khalil (ya rasu)
3. Abubakar Sadiƙ (ya rasu)
4. Junaidu (Nakuci)
5. Muhammadu Bello
6. Barrister Muhammadu Lema
7. Dakta Muhammadu Mustapha
8. Ja’afarus Sadiƙ
9. Harun Arrashid
‘Ya’ya Mata
10. A’ishatu (ɗiyar ‘Yan Mamma)
11. Asma’u (Jamila)
12. Labratu
13. Hajaru
14. Khadijatu
15. Fatimatu
16. Zainabu
17. Ruƙayyatu
18. Hafsatu
19. Halimatus Sa’adiyya (ta rasu).
Duka-duka, Allah ya bai wa Muhammadu Sambo Wali ‘ya’ya goma sha tara ne, sai dai akwai huɗu (Ibrahim, Abubakar, Labratu, Halimatus Sa’adiyya[15]) waɗanda suka rasu. Yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar ne a raye.
Mallam Sambo Wali ya rasu ranar Talata 24 ga watan Yuni, 2025 miladiyya wanda ya yi daidai da 29 ga watan Zul-Hijja 1446 hijiriyya, bayan kwashe kimanin shekaru goma yana jinya. Duk da wannan jinya da ya yi da kuma yanayi na tsufa, Allah bai sa hankalinsa da tunaninsa sun gushe ba. A cikin wannan yanayin na tsufa da jinya mutane sukan je wurinsa domin neman tarihi da tuna musu abubuwa da dama da su kansu sun kasa tunawa.
An yi jana'izarsa a cikin gidan Sarkin Musulmi, aka kuma turbuɗe shi a Hubbaren Shehu Usmanu dan Fodiyo cikin garin Sakkwato.
Da fatar Allah ya saka masa da alheri, ya gafarta masa, ya sa aljanna ce makomarsa. Amin[16].
Wasu daga cikin Ayyukan Mallam Muhammadu Sambo Wali
Waƙoƙinsa Na Ƙarni Na Ashirin (Ƙ. 20)
1. Waƙoƙin Addini
· Tauhidi Nazari
· Roƙon Allah
· Yabon Annabi (SAW)
· Addu’a
2. Waƙoƙin Tarihi
· Tarihin Hijirar Shehu Da Kafa Daular Usmaniyya
· Waƙar L.G.R. 1975
3. Waƙoƙin Wayar Da Kai
· Waƙar IFAD
· Amfanin Shukka Itace (bishiyoyi)
· Gasar Noma
· Tahamisin ‘Gona da Mallan’
· Lafiya Uwar Jiki
· Matakan Kirkin Jiharmu
· Na Fara Kiran Ku ‘Yan Yara
4. Waƙoƙin Gargaɗi
· Gargaɗi
· Gargaɗi Kan Gurgusowar Hamada Da Zaizayar Ƙasa
· Gaskiya Mugunyar Magana
· To Da Ke Nike
· Shaye-Shaye Aibi Na
5. Waƙoƙin Faɗakarwa
· Ku Bar Zaman Banza Da Barace-Barace
· Shirin Zamani (Tahamisi)
· Kishin Ƙasa
· Yaƙi da Jahilci
6. Waƙoƙin Siyasa
· Gidauniyar Jihar Sakkwato
7. Waƙoƙin Yabo
· Jamborodo (Tahamisi)
8. Waƙoƙin Soyayya
· ‘Yarkiɗi
9. Waƙoƙin Talla
· Waƙar Omo
· Waƙar King Cola
· Kamfanin Westek
· Kamfanin Haji Yaro Boɗinga
10. Waƙoƙin Nishaɗi
· Naira Alfarmar Zamani
11. Sauran Waƙoƙi
· Tsangwama da Gunaguni
· Ƙalubale Ga Masu Sukar Shan Taba-gari
Waƙoƙinsa Na Ƙarni Na Ashirin Da Ɗaya (Ƙ. 21)
1. Waƙoƙin Tarihi
· Tarihin Masarautar Gwandu Ta Gidan Hassan Ɗan Abdullahi
· Bin Shari’a Da Adalci Su Ne Kayan Adon Masarautar Gwandu
· Tarihin Zabarmawa Da Ƙasarsu Ta Asali Da Sunan Kakansu
· Gudummuwar San’inna Gari-Hanaye Ga Jihadin Shehu
· Tunawa Da Ayyukan Maimartaba Sarkin Argungu Muhammadu Mera
2. Waƙoƙin Wayar Da Kai
· Shan’inna (Polio)
· Bunƙasa Ayyukan Noman Fadama
· Kula da Lafiyar Mata Da Ƙananan Yara
· Cika Alƙawali Aikinka Na
3. Waƙoƙin Faɗakarwa
· Mu Jajirce Ga Aikin Gayya
· Ku Tashi Da Himma Maza Zuwa Aikin Gayya
· Zaman Lafiya
4. Waƙoƙin Siyasa
· Ranar ‘Yancin Nijeriya
· Taya Sarkin Yamma Aliyu Magatakarda Wamakko Murnar Zama Gwamnan Sakkwato
· Albishirin Matafiya Gwamnatin Sarkin Yamman Daular Usmaniyya
· Nasarorin Aliyu Magatakarda Wamakko
· Ba A Taɓin Maza Su Koma Su Yi Kwance
· Ga Ƙasa Samun Abin Ƙwarai Dace Na
5. Waƙoƙin Yabo
· Du’a’i Ga Mai’alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar Na’ukku
· ‘Zauren Waƙa’ Muhimmi Na
· Manufofin Hassan Kangiwa
Rubuce-Rubucen Mallam Muhammadu Sambo Wali Na Tarihi
1. Shigowar Fulani Ƙasar Hausa Da Kyakkyawar Zamantakewarsu Da Haɓe
2. Gobirawa Da Asalinsu
3. Tarihin Gimbanawa
Taƙaitaccen Tarihin Masarautar Jega
Taƙaitaccen Tarihin Mallam Abdussalami Bagimbane
Wasiccin Jada Maijega
Tarihin Gidan Mujahidu ɗan Abdussalam
Tarihin Dangantakar Dagelawa da Sambawa da Gimbanawa
4. Asalin Hausawa Ga Tarihi
5. Tushen Arawa Tun Daga Abuyazid (Bayajida)
6. Asalin Kanta Ɗan Makata Ɗan Kotai
8. Tarihin Sissilɓe (Sulluɓawa)
9. Tarihin Ƙasar Yauri A Taƙaice
10. Faɗakarwa A Kan Haɗin Kan Musulmi Da Matsayin Bara Da Raraka A Musulunci
[1] Ta dalilinsa da jama’arsa ne aka fara jihadin jaddada addinin Musulunci a ƙasar Hausa. Duba ‘Tarihin Abdussalami Bagimbane’ na Muhammadu Sambo Wali.
[2] Saboda birnin Alƙalawa asalinsa na Gimbanawa ne. Gobirawa suka yi musu zamba-cikin-aminci suka ƙwace birnin. Wato bayan sun ɗauki lokaci mai tsawo a ƙasar Agadez, Attawariƙ (Buzaye) na kashe musu sarakuna har kusan guda hamsin, sai suka gudo suka yo birnin Kunya (yana cikin Damagaram, Nijar yanzu), inda Sarkin Borno Mai Ari ya ba su mafaka. Daga nan kuma suka yo ƙasar Hausa, inda Sarkin Zamfara ya ba su mafaka cikin birnin Lalle (yana cikin Madawa, Nijar yanzu) kusa ga birnin Alƙalawa. To, daga nan ne bayan sun saki jiki, sai suka yi ta yunƙurin cin birnin da yaƙi kimanin shekaru goma shatakwas, amma ba su sami nasara ba. Suka yanke shawarar yin amana da Gimbanawa. Bayan an yi amanar, sai suka yi zamba-cikin-aminci, suka auka wa birnin a daidai lokacin da Gimbanawa suke gona, suna noma. Suka ƙwace birnin ba tare da wata wahala ba. Duba ‘Tarihin Gobirawa Da Asalinsu’ na Sambo Wali, domin ƙarin bayani.
[3] Shi ne waziri na shida a tsarin wazirran Sakkwato. Ya yi wazircin daga 1910 zuwa 1912 miladiyya.
[4] Shi ne waziri na farko a Sakkwato bayan Shehu Abdullahi ɗan Fodiyo ya koma Gwandu. Ya yi wazirci daga 1817 zuwa 1842. Ya rasu a shekarar 1850 miladiyya. Duba Jean Boyd da Beverly B. Mack The Collected Works of Nana Asma’u: Daughter of Usman ɗan Fodiyo (1793 – 1864) (1999; Nigerian Publishing) shafi na 228.
[5] Futa-Toro na cikin ƙasar Senegal a Afurka Ta Yamma.
[6] D.O (District Officer) wato Jami’in Gunduma.
[7] Cikakken sunansa shi ne Mr. Neil Skinner. Baturen Ingila ne ɗan Mulkin Mallaka. Shi ne ya rubuta Kamus Na Turanci Da Hausa (English – Hausa Illustrated Dictionary): Babban Ja-gora ga Turanci (1965).
[8] National Broadcasting Corporation.
[9] Sabon sunan da aka sa wa gidan rediyon ke nan a 1979. Kuma Sambo Wali ne ya ba shi wannan suna bisa ga dalilan cewa, birnin Zamfara yana bisa ga Gulbin Rima. Alƙalawa birnin Gobirawa yana bisa ga Gulbin Rima. Sakkwato da Wurno manyan biranen Daular Usmaniyya suna bisa ga Gulbin Rima. Gungu da Surame manyan biranen Kanta suna bisa ga Gulbin Rima. Birnin Kabi da Argungu biranen sarautar Kabawa kashi na biyu, suna bisa ga Gulbin Rima.
[10] Centre for Islamic Studies, UDU, Sokoto.
[11] Lokacin da tsufa ya kama shi da kuma rashin isasshiyar lafiya.
[12] Wadda ya yi a 1951, wato yana da shekaru 14.
[13] Alhaji Iliyasu Bashar.
[14] Ni kaina na rubuta guda biyu na haɗaka. Ɗaya a cikin harshen Hausa, ɗaya kuma a cikin harshen Ingilishi. Ga sunayensu kamar haka:
1. ‘Muhammadu Sambo Wali (Basakkwace): Gudummawarsa Ga Ci Gaban Adabi Da Tarihi’. Maƙalar da aka gabatar a Taron Ƙasa-da-Ƙasa na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci da ke Jami’ar Bayero, Kano game da ‘Matsayin Fasaha ga Ci Gaba’ [The Role of Art to Development]. (Sambo, A.W. da Alfanda, A.A.
2 ‘The Role of Hausa Written Poets in Conflict Resolution: A Case Study of Sambo Wali Giɗaɗawa’ [Rawar da Marubuta Waƙoƙin Hausa ke takawa wajen samar da Zaman Lafiya: Nazarin a kan Sambo Wali Giɗaɗawa]. Maƙalar da aka gabatar a taro na 31 na Ƙungiyar Manazarta Kimiyyar Harshe ta Nijeriya (Linguistic Association of Nigeria) a Jami’ar Ilimi ta Ignatius Ajuru da ke birnin Fatakwal, jihar Rivers. (Ahmad, A.A. da Sambo, A.W. 2017).
[15] Ta rasu ranar 17 ga Okotoba, 2016.
[16] Dakta Almustapha (Mujtaba) Sambo Wali ya rubuta wannan tarihi tare da taimakon mahaifinsa Sambo Wali a ranar Alhamis 11 ga Agusta, 2016 Miladiyya, daidai da 8 ga Zulƙi’ida, 1437 Hijiriyya. An sabunta wannan tarihi bayan rasuwarsa a ranar Assabar 29 ga Yuni, 2025 Miladiyya, daidai da 3 ga Muharram, 1447 Hijiriyya.
0 Comments